Pulse logo
Pulse Region

Tsohuwar jaruma Mansura Isa tayi bikin murnar ranar haihuwar ta tare da nakasassu (Hotuna)

Iayalai da abokan arzikin sun taya tsohuwar jarumar murna ina tayi bikin nuna farin cikin wannan muhimmiyar ranar tare da guragu a jihar Kano

Tsohuwar jarumar Mansura ta kara shekara daya a duniya jiya lahadi 25 ga wata kuma nuna farin cikin ta bisa kaunar da yan uwa da masoya suka nuna mata tare da sakonnin farin ciki da suka tura mata.

[No available link text]

*Matan Kannywood da suka nishadantar da al'umma shekarun baya

Mansura tayi bikin frin cikin zagayowar wannan muhimmin ranar tare da iyalenta da abokan arzikin a zauren nakasssu guragu dake nan Nasarawa a jihar Kano.

*Hanyar da mata zasu bi wajen mallakar miji (Bidiyo)

Manyan jarumai da suka halarci wannan bikin domin taya ta murna tare da guragun sun hada da mai gidanta Sani Danja da Yakubu Muhammed da Mustapha Naburiska da babban mai shirya fim Umar Gombe.

Uwar dakin jarumi Sani Danja, ta samu yabo daga dimbin masoyanta inda suka jinjina mata bisa taimakon da take baiwa nakasassu mara galihu ta hanyar gidauniyar ta Todays life Foundation.

Subscribe to receive daily news updates.

Next Article