Ya sanar da anniyarsa na neman zarcewa a zaben nan gaba ranar 9 ga wata a taron jiga-jigan jam'iyar APC jim kadan kafin ya bar kasar zuwa Ingila inda ya kai ziyarar aiki.
Shugaban yace ya sanar da kudirin tsayawa takara domin katse cece-kuce da yan kasa keyi kan batun ko zai nemi zarcewa wanda hakan ya sanya anyi watsi daga muhimman batutuwa wadanda ya kamata a sa gaba.
Yayi wannan ikirarin yayin da karbi bakoncin amininshi kuma babban limamin cocin Centebury, Justin Welby a birnin Landan ranar laraba 11 ga watan Afrilu.
"Na yanke shawara ne kafin na bar kasar ganin yadda yan Nijeriya suka mayar da hankali kan batun zan nemi zarcewa ko kuma akasin hakan. Akwai muhimman batutuwa da ya kamata mu mayar da hankali akai musamman a bangaren tsaro, noma, kasuwanci, yaki da cin hanci da sauran su. Wadannan batuwan ya kamata mu mayar da hankali akai ba kan siyasa ba. Mafi yawancin yan Nijeriya sun gamsu da ayyukan da gwamnatin mu keyi, wanan shima yana cikin dalilin da yasa zan nemi zarcewa" Shugaban ya shaida ma amininsa Justin Welby.
* PDP bata fargaba kan wa'adin shugaba Buhari na tsayawa takara
Game da ta'adanci dake faruwa a kasar, shugaban yace ana kokarin wayar da kan al'umma musamman a fanin ilimi/karatu domin mai ilimi baya ba za'a wayence masa ba. Ya kara da cewa babu addinin dake goyon bayan kisa ko raunata dan Adam.
Game da rikicin makiyaya da manoma, Shugaba Buhari ya shaidawa amininsa cewa tsohon Shugaban Libya, Marigayi Mu'ammar Ghaddafi ne ya horas tare da bayar da makamai ga wasu makiyaya wanda baya kifar da mulkinsa, shi ne suka arce kuma suka shigo Nijeriya suna aikata ta'addanci.
Buhari ya nuna cewa a can baya an san makiyaya suna dauke da sanda ne a maimakon yanzu, da ake ganin su da manyan bindigogi inda ya nuna takaicinsa kan yadda shigo da siyasa cikin wannan rikici na makiyaya da manoma wanda rikici ne mai dogon tarihi.