Tayi wannan kiran ranar litinin a garin Kano yayin da yan majalisar dattawa suka hada wani gaggarumin taro kan amfani da miyagun kwayoyi.
Tace Nijeriya na bukatar kwakwarar yaki da amfani da miyagun kwayoyi kuma tayi kira na a lura da yanayin yadda ake safarar magunguna a biranai da kananan hukumomi.
"Ya kamata jama'a da sarakunan gargajiya da cibiyoyin kula da masu tabin hankali su hada gwiwa wajen yakar yawan amfani da miyagun kwayoyi a jihohi da ma kasar baki daya"tace.
Shima wani jigo a hukumare NAFDAC Dr Umar Usman ya jaddada kan batun inda shima yayi kira ga jama'a da su taimaka wajen ganin an cinma burin yakar amfani da miyagun kwayoyi a fadin kasar.
"Ya kamata a hukunta duk wani mai sayar da magunguna irein su Codein ga matasa domin su zama abun lura ga sauran masu ire-iren sana'ar"yace.