Pulse logo
Pulse Region

Malam Mai rakumi ya samu hukuncin shekaru goma a gidan yari

Mai shari'a Lewis Allagoa ya zartar da hukuncin Mai rakumi  a zaman da aka yi ranar Alhamis bayan da aka kama shi da laifin mallakar kudin bogi.
___9088247___2018___11___9___12___bogi
___9088247___2018___11___9___12___bogi

Kotu tarayya dake gudanar da zaman ta  jihar Kano ta hukunta shahararen malami mai aiki da rauhanai, Abubakar Ishaq, wanda aka fi sani da Mai rakumi da hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari.

Mai shari'a Lewis Allagoa ya zartar da hukuncin Mai rakumi  a zaman da aka yi ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba bayan da aka kama shi da laifin mallakar kudin bogi.

Alkalin sa, Barrister Mohammed Aliyu, ya nemi kotu ta maidawa malamin hukuncin daurin zuwa shekara tara. Sai dai mai shari’a Allagoa ya ki amincewa da hakan.

Alkalin ya kuma nemi a lalata kudin jabun da aka samu wajen babban Malamin.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar dashi bayan da hukumar NDLEA ta cika hannu dashi  bayan kama shi da mallakar makudan kudi dalan Amurka na bogi bayan da tayi bincike a gidan sa.

Next Article