Pulse logo
Pulse Region

Sirri 5 da ya kamata ku sani game da wanda ya lashe big brother naija, Efe

Bayan an yi watanni da kallon Efe, har yanzu akwai abubuwa da ba ku sani ba game da Efe.
Efe during his diary session
Efe during his diary session

An yi watanni hudu, 'yan Nijeriya na kallon Efe da kuma sauran yan takara zaune a cikin wani gida, da kuma yaƙin ƙoƙarin samun babban kyauta, shahara da kuma wani dandali na samun ci gaba a sana'arsu.

Da farko a cikin shirin, Efe ya sanar da kansa tare da ƙasƙantar da kansa. Masu sauraro sun ƙaunace shi. A lokacin Big Brother so ɗaya a ka kusa korar shi. A ranar fitar lahadi, ƙuri'un Efe bisa dari shine mafi yawa,ya nuna cewa zai lashe shirin.

A ƙarshen shirin, ba abun mamaki bane da aka ayyana Efe da cin nasara. Ya ja 57,61%  na zaɓen da aka haɗa, kashi uku bisa ga abun da Bisola ta samu, ita ce mai biye ma Efe.

Kun yi kallon Efe a ƴan satin baya, amma ta yaya kuka san wanda ya lashe Big Brother Naija, ga abubuwa 5 game da Efe.

  • Efe dan shekara 24 ne, an haife shi a Fabairu 25, 1993, ya na da tausayi, kyakkawar ɗabi'a, hikima, kuma yana son waƙa.
  • Efe ɗan Warri ne, a jihar Delta ,jihar da ta samar manyan jaruman Nijeriya kamar Richard Mofe Damijo, Omawumi, Bovi da sauransu.
  • Efe mawaƙi ne mai yin waƙar 'rap", a watan Oktoba 2016 ya fito da wani EP mai laƙani 'Lagos', Jikin aikin na da waƙoƙi guda 14.
  • Efe ya kammala karatu a jami'ar Jos, inda ya yi karatun tattalin arziki.
  • Wizkid ma'aboci na Efe ne. har maganar sa a cikin Big Brother  "Based on Logistics" ya zama sananne sosai har Wizkid ya rubuta a shafin sa na twitter.
Next Article