Pulse logo
Pulse Region

Daga karshe, shugaba Buhari zai tsaya takara a zaben 2019

Shugaban ya sanar da haka a taron shugabannin jam'iyar APC dake gudana a hedkwatar jam'iyar dake Abuja

Wannan labarin ya fito a wata sanarwa da hadimin sa Bashir Ahmad ya fitar a shafin sa na kafar sada zumunta ta twitter.

Bashir ya rubuta cewa shugaban ya amince da neman zarcewa a kujerar mulkin kasa. A bayanin da ya wallafa, za'a fitar da karin bayanai kan matakin da ya dauka nan ba da jimawa ba.

Shima gwamnan jihar Kaduna  malam Nasir El-rufai ya tabbatar da labarin inda ya nuna farin cikin sa a sakon da ya wallafa a shafin sa na twitter.

Shugaban ya sanar da haka a taron shugabannin jam'iyar APC da aka gudanar safiyar yau.

Next Article