Ƴan Sandan Nijeriya a ranar Litinin, Maris 8, ta ce an kama mutane 21 waɗanda ake zargi game da kashe-kashe da lalata dukiya a Ile Ife, Jihar Osun.
Ƴan sanda sun tsare mutane 21
Kakakin ƴan sanda, Jimoh Moshood ya bayyana haka a Abuja a lokacin da ya gabatar da waɗanda ake zargi a gaban ƴan jarida.
Kakakin ƴan sanda, Jimoh Moshood ya bayyana haka a Abuja a lokacin da ya gabatar da waɗanda ake zargi a gaban ƴan jarida.
Ya ba da sunayen su kamar haka, Eluwole Akeem, Kuburat Eluwole, Ayoola Abimbola, Bello Wahab, Taiwo Fakuwajo, Ademola Ademiluyi, Peter Omisope, Adefisan Isaac, Adelekan Kehinde da Elufisan Akintoye.
Sunayen sauran na kamar haka, Omisanmi Isaac, Olanrewaju Daniel, Seyi Akinyobo, Adejube Monday, Olanrewaju Adebayo, Akanbi Adeyinka, Obimankinde Samuel, Zakariyu Abdulyekini, Bamidele Elusanmi, Jimoh Sakiru da Clement Kehinde.
Ya bayyana cewa, mutane 39 da ake zargi aka kama bayan rikicin, aka saki 18 bayan bincike domin rashin shaida, a kansu.
Moshood ya ce, sauran 21 da aka kama, an gan su da laifin tsoma hannu kai tsaye a kisan mutane.
Ya lura da cewa jami'an tsaro na musamman da aka tura zuwa Ile-Ife domin kwantar da rikicin ba su kama kowa da rashin la'aƙari ba, kamar yadda ake bayar da rahoton a wasu kafofin watsa labarai.
Ya ce rikicin ya fara a kan Maris 7 a lõkacin da ƙungiyoyin Yarabawa da Hausawa suka fara jefa wa juna duwatsu, waɗannan ake zargi da fara rikicin, Kuburat Eluwole da Abubakar Mohammed.
"An tarwatsa masu tarzoman, an kwantar da hankalin kowa da kowa"
Ya nuna cewa ƴan sanda sun jira a gaban yankin Sabo a Ile-Ife har kashegari.
Ya shawarci sarakuna, da shugabannin addini, ƴan siyasa da kuma iyaye su goyi bayan ma'aikatan jami'ar tsaro na musamman a jihar.
Ya ce za a gurfanad da waɗanɗa aka kama a gaban shari'a a kan kammala bincike, yayin aka sake mutane 18.
Inspector General na 'ƴan sanda, Mr Ibrahim Idris, ya tura' ƴan sanda (SIF) zuwa Ile-Ife, Osun, don mayar zaman lafiya a yankin
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng