ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Alamun ciwon zuciya ga jikin Mata

Ciwon Zuciya yana da haɗari sossai, kuma akwai bambaci ga alamun bayyana cututtukka tsakanin macce da Namiji.

Alamun ciwon zuciya ga jikin Mata

Ciwon ƙirji yana cikin nagartaccen alama na gane farawan ciwon zuciya. Ciwon zai iya miƙa har zuwa hannu guda a cikin Namiji. Amma idan macce tana da ciwon zuciya, akwai yiwuwar cewa alamun zai kubuce mutum, domin wuyan ganewa a jikin mata.

Wadannan alamu na ciwo zai bamu hasken gane farko na ciwon zuciya a Mata.

1. Ciwon Ƙirji

ADVERTISEMENT

Ciwon Ƙirji ɗaya ne daga cikin alamomin farawan ciwon zuciya a cikin ʼmacce. Wannan ciwo yana zuwa da rashin jin daɗin jiki da kuma jin matsewan ƙirji. Wani lokaci, ana jin wuyan numfashi a kowane ɓangaren ƙirji.

2. Jin Juya da alamun suma.

Idan mace tana da Ciwon Zuciya, za ta riƙa jin kaman tana juyawa idan ta miƙa tsaye. Juya ɗin zai zama mai nace ko da yaushe. Wannan alamar ne cêwa bugun jini yana kusa.

3. Gajiya

Gajiya babban alama ne na farokon ciwon zuciya. Jin gajiya sossai, ba tare da wani aiki ko wani dalili, ko wani motsan jiki yan ciki alamar ciwon zuciya.

ADVERTISEMENT

4. Ciwon ciki.

Rashin jin daɗin ciki yana cikín alamar ciwon zuciya ga mata. Wannan ciwo zai kasance da matsa lambu da damuwan yanayi na ciki.

4. Ciwon Wúyà, Bayá da muƙamuƙi.

Idan ana neman alamomin ciwon zuciya ga macce, a lura da ciwon Muƙamuƙi, wuya, da ciwon baya. Macce za ta ji tasowan waɗannan ciwon za tu taso haka ɗai kawai, ba tare da dalili ko wani motse-motse na jiki. A wasu lokuta, wannan ciwon zai yi yawa a ƙasa ga hannun dama na muƙamuƙi.

5. Rashin numfashi mai kwari.

ADVERTISEMENT

Idan macce tana jin rashin issahen numfashi, akwai alama cêwa tana da ciwon zuciya, har dai idan wannan ciwo yana karuwa a lokacin da ta na kwance. Haka kuma idan ta tashi tsaye, wannan ciwon zai rage. Wani lokaci, a kan yi zufa sossai, da kuma kumallo.

A lura da waɗannan alamomi domin kiyayewa. Idan aka lura da kowane daga cikin alaman, a koƙarta a bincike likita domin ƙarin nazari.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT