ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ku dena haihuwan ʼƴaʼƴa kamar kayyayaki

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya roki yan Arewa su canza halayensu game da aure, da haihuwa.

Ku dena haihuwan ʼƴaʼƴa kamar kayyayaki

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya roki yan Arewa su canza halayensu game da aure, da haihuwa. Sarki ya bayar da wannan shawara a lokacin da yake jawabi a ranar cika shekaru sittin na Makarantar Capital School na garin Kaduna.

Sarki Muhammadu Sanusi ya shawarce ƴan Arewa su auri yawan matan da suke da ƙarfin biyan buƙatansu, kuma ya dage cêwa bai kamata mutane su haife yara masu yawa har dai idan basu da halin samar da su. Ya buƙaci mutane su ɗauki wannan shawara domin ci gabansu da na Alʼummah, da kuma Arewa gaba ɗaya.

Da yake jawabi a ranar lacca na tunatarwa da Wanda ya kafa makarantan Capital School, Sarki Sanusi ya bayyana cêwa ya zama wajibi ga shuagabanni, su ilmantar da Alʼummah akan manufofifn alʼumma. Sarki ya nanata cêwa baya jayayya da duk wanda ya auri mata da yawa, da kuma haihuwan yara masu yawa, har dai idan yana da issashen albarkatu na kula da su.

Ya yi kalamai haka:

ADVERTISEMENT

"Za ka iya ka auri mata biyu idan kana da hali na kula da su. Za ka iya ka haife yara ɗari idan ka na da ƙarfin biyan buƙatunsu, da kuma ƙarfin ilmantar da su; Amma idan ba ka da hali, ka auri mata daidai da iyawanka, kuma ka haifi yara daidai da bakin iya kula da su."

Ya cê yara waɗanda suka samu issashen kula da ƙaunar iyayensu, su ne ke zama masu darraja ga kansu, da kuma Alʼummah gaba ɗaya.

"Mun damu da haihuwan yara masu yawa. Duk abinda ka tara da yawa, zai zama abin arha. Muntane sun haifi yara da yawa kaman kayayyaki, yara suna saman tituna kuma suna mutuwa ba tare da damuwan mutane domin basu da darraja. Yawancin yaran sun shiga harkan shaye-shaye, kuma mutane sun kauce fuska." Sarki ya jaddada.

Sarki ya umurce shuagabanin Arewa cêwa su ɗauki matakai cikin gyaggyawa domin bincikar kasawar manufofin alʼummah a arewancin najeriya. Ya yi umarni na bincika matsalolin saurin aure, halayen mutane ga harkan aure, auren mata fiye da ɗaya, tsarin iyali,  kashe aure, hakin yara akan iyayensu, hakin iyaye ga yaransu, da sauransu.

Sarki ya cê  mutane da yawa a Arewa sun ɗauka cewa Uba kawai yake da wajibin kula da yara. Ya nemi goyon bayan ƙungiyoyi da ƴan kasuwa masu zaman kansu. Ya gayyaci "Mallamai da ƙungiyoyi su mayar da hankali akan manufofin alʼummah, ginin makaranttu, horon Malaman Makaranta, samar da kayan aiki da kuma bayar da malanta/sukolashif domin amfanin ɗalibai"

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT