ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaba ya riga ya faɗa muku cewa ba ya da lafiya

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo a Maris 10, daga hutun kwana 49 inda ya je duba lafiyarsa a London.

Shugaba ya riga ya faɗa muku cewa ba ya da lafiya

Ministan Bayanai, Lai Mohammed ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna ƙalubalen Lafiyarsa a FIli tun watan Maris.

Shugaba a lokacin ya ce, bai taɓa irin wannan rashin lafiyar a duk rayuwarsa ba.

Shugaba ya shaida wa dukkan ƙasa cewa, bai taɓa irin wannan rashin lafiyar ba, kuma zai yi a hankali," Mohammed ya faɗa wa ƴan jarida a gidan shugaba a ranar Laraba, May 3, bayan taron FEC da Buahri bai kasance ba.

Ya faɗa tun ranar da ya dawo daga UK, Saboda haka duk abun da ya taso yau ba sabon labari bane, abun da ya ce - likitocin sa sun ce masa ya yi a hankali, kuma ƴan lokuta kadan zai koma domin cigaba da jinya.

ADVERTISEMENT

"Ban yi tunanin akwa banabanci a cikin abubuwan da ya faɗa ba, ya nuna a fili abubuwan da suka shafe lafiyarsa," ya ce.

Mohammed ya ce a Afrilu 26, bayan rashin kasancewar Buhari a taron FEC na ranan, wai Shugaba zai yi aiki daga gida saboda ya na buƙatar hutawa.

Duk da haka, a Afrilu 12, Mohammed ya Bayyana rashin kasancewar Buhari a taron FEC a matsayin ya na da wasu lamurra masu muhimmanci da ya kama ya duba.

Buhari bai je taron FEC ba so uku tun Afrilu 12, abun ya ba da tunanin cewa ya koma rashin lafiya.

Matar Shugaba Aisha, a ranar talata 2, ta ce ƙalubalen lafiyarsa bai yi munin yadda mutane ke tunani ba.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT