ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An Kashe Uwa da ƴa'ƴan ta Biyu da nakiya a Jihar Borno

A lokacin da ƴan ta'addan suka gane cewa an gane su, sai suka watsa hanyoyi daban-daban, sannan suka tada na'urar dake maƙale a jikinsu yayin kan gudu.

An Kashe Uwa da ƴa'ƴan ta Biyu da nakiya a Jihar Borno

Akalla an ruwaito mutane bakwai matattu bayan ƴan ta'adda guda uku sun kai farmaki a wani ƙauye a Maiduguri, Jihar Borno.

Wata Uwa, ƴaƴanta biyu, da kuma wasu mutane huɗu sun rasu akan harin da ya faru a daren Asabar, Maris 18. An ce maharan sun yi yunƙurin shiga Maiduguri ta ƙauyen Umarari a Molai, inda ƴan Civilian Joint Task Force (CJTF) suka ƙalubanta su.

A lõkacin da suka gane cewa ya na yiwuwa an gane su, sai suka watse a hanyoyi daban-daban, suka tada nakiyoyin da ke maƙale a jikinsu yayin kan gudu.

Wasu mutane Takwas sun ji rauni a harin, su na ƙarbar magani a wani asibiti a garin.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT