ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

kada ku je Amurka, sai in dalilin zuwa mai muhimmanci ne

Dabiri-Erewa ta bayyana wannan gargaɗin, bayan an hana wasu ƴan Najeriya masu takardar izinin zama Amurka shiga.

Abike Dabiri,  Senior Special Assistant to President Muhammadu Buhari on Foreign Affairs and Diaspora

Babban musamman mataimakin Shugaba Muhammadu Buhari, a harkar ƙasar waje, Dabike Dabiri-Erewa ta buƙaci ƴan Najeriya kada su yi tafiya zuwa Amurka sai har in dalilin zuwa na da muhimmanci.

Dabiri-Erewa ta bayana cewa gargaɗin ya zama dole, bayan an hana wasu ƴan najeriya masu takardar izinin zama shiga Amurka.

Ta sanya wannan magana a wata sanarwa da  mataimakin ta na kafofin watsa labarai, Abdurrahman Balogun ya sake.

Sanarawan: a satin baya, ofishin mu ya samu wasu rahotanni cewa an hana wasu ƴan najeriya masu takardar izinnin shiga Amurka shiga kasar, ana korar su zuwa najeriya.

ADVERTISEMENT

A rahotannin da ake kawowa a ofishin mu, mutanen da ya shafa, an kore su nan take, da zuwar su aka sa su a jirgin sama, sannan aka soke takardar izinin zaman su a Amurka, babu bayani ko hujja.

Ta ƙara cewa, wannan sanarwan domin ba “ƴan Nijeriya shawara cewa duk wanda ba shi da dalili mai muhimmanci da zai kai shi Amurka, ya canza lokacin zuwa, har a sasanta da sabuwar dokar shige da ficen Amurka.”

Sabon Shugaban ƙasa Amurka, Donald Trump ya sha suka akan sabon doka na shige da fice da ya ke son sawa, domin hana musulmai shiga ƙasar.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT